✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana sa-in-sa tsakanin Sarkin Sasa da ’yan kasuwar Sasa a Ibadan

Wata rashin jituwa a kwanan nan ta faru tsakanin ’yan kasuwa a Kasuwar Sasa Ibadan da kuma Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin, inda al’amarin ya…

Wata rashin jituwa a kwanan nan ta faru tsakanin ’yan kasuwa a Kasuwar Sasa Ibadan da kuma Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin, inda al’amarin ya haifar da tsegunguma da korafe-korafe a tsakani. 

Domin bin kadin al’amarin da abin da ya haifar da shi, wakilin Aminiya ya gana da dukkan sassan biyu, inda Shugaban kungiyar ’Yan Kasuwar Gwari ta Sasa a Ibadan, Alhaji Usman Yako ya ce suna zargin sarkin na Sasa ne da yin amfani da jami’an tsaro wajen takura masu. “Duka ’ya’yan kungiyarmu Hausawa da Yarbawa, mun dauki Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin a matsayin Sarki mai jagorancin jama’arsa bisa kyakkyawar hanya amma ba mai danne hakkin talakawansa ba. Sau da yawa yana yi mana abubuwan da suka saba da sarauta domin muna zargin yana hada baki da jami’an tsaro da suke zuwa suna takura mana suna kulle mu ba gaira ba dalili. Abun da muka sani da Sarakuna shi ne suna yin aikin kwato hakkin talakawansu ne ba akasin haka ba,” inji shi. 

Ya kara da cewa: “Sarkin Sasa ba ya harkar kasuwanci, su ma ’ya’yansa ba su saye ko sayarwa a cikin kasuwar , amma sai shafa mana kashin kaji yake yi cewa mu ’yan Boko Haram ne. Idan jami’an tsaro suka yi bincike sai su gane cewa matsalar da ta shafi kasuwa ce a tsakaninmu, babu ruwanmu da ’yan ta’adda. Muna so Sarkin Sasa ya rike sarautarsa, mu kuma za mu yi masa biyayya, ya daina yin katsalandan a cikin harkokin kasuwancinmu; domin babu ruwansa da harkar kasuwanci kuma ya daina turo jami’an tsaro suna kama mu haka kawai.”

A game da ikirarin cewa Sarkin Sasa ne ya kafa wannan kasuwa shekaru 39 da suka wuce amma kungiyarsu ta ki ba shi hadin kai domin samun ci gaban kasuwar, sai shugaban ya ce: “Abin da muka sani a gwamnatance a kasar nan, ba mu taba jin wani mutumin da yake ikirarin cewa shi ne ya kafa ko ya mallaki wata kasuwa ba sai a nan Sasa.”

Aminiya ta tambaye shi hanyar sasanta tsakani, sai Usman Yako ya ce: “Mu ’yan kasuwa ne ba fada muke yi da shi ba. Shi kuma Sarki ne yake yin amfani da wannan dama wajen shiga harkar da ba ta shafe shi ba. Kamata ya yi ya kyale mu da kasuwancinmu, ya ji da sarauta. Yin haka ne zai kawo karshen wannan matsala.”

A nasa bangaren, Shugaban Majalisar Sarakun Hausawa a Jihohi 17 na Kudancin kasa, Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin, ya ce: “Wannan kasuwa ta Sasa, ni na same ta shekaru 39 da wucewa na gyara ta, na kwaso jama’a Hausawa da Yarabawa na kawo suka fara kasuwanci a cikinta. Wadannan ’yan tsiraru da suke neman tayar da kayar baya, babu su a wancan lokaci. Shugabannin kasuwar a yanzu suna jayayya ne da ’ya’yana da suka kora, su suka ki amincewa su kasance a cikin kwamitin da mahukunta suka kafa domin lura da kasuwar.

“Ba da ni suke jayayya ba, domin babu abin da ya hada ni da jayayyar kasuwa; domin ni ba dan kasuwa ba ne kuma duniya kowa ya sani cewa, ni Sarki ne shugaban al’umma,” inji shi.

Ya kara da cewa: “A daidai lokacin da kasuwar take hada-hada a wancan lokaci sai wadannan ’yan kasuwa (Hausawa) suka hada kai da wasu Yarabawa, suka kai kara ta ga ’yan Majalisar Dattijai, wdaanda suka kira ni domin yin bayanin abin da ke faruwa. Na je tare da Baale na garin Sasa ne, a inda na yi masu cikakken bayani, inda a nan take ’yan Majalisar Dattijan suka tabbatar da cewa garin Sasa yana karkashin Baale ne amma kasuwa tana karkashin Sarkin Sasa ne.

“A yayin da ’yan majalisar suka tambaye ni mafita a kan wannan al’amari, na gaya masu cewa komai yana hannunsu ne tun da sun kira ni. A nan ne suka nemi amincewa ta domin kafa kwamitin da aka rantsar da su domin lura da harkokin kasuwar na tsawon shekara 3 da zai kammala aiki. Akwai wakilaina da wakilan Baale a cikin wannan kwamiti, amma abin mamaki sai wadannan ’yan kasuwa suka ki amincewa da kasancewar ’ya’yana a cikin kwamitin, suka kore su daga kasuwar baki daya.

“Yaran nawa da abokansu sun zo gare ni a fusace domin sanar da ni abin da ya auku tsakaninsu da ’yan kasuwa. A nan take na ba su hakuri kuma na umarce su da su amince da daukar wannan mataki har zuwa karshen shekara 3 da wa’adin kwamitin zai kare. Bayan wannan ne aka sake kafa wani kwamiti da ’yan kasuwar suka ki amincewa da daya daga cikin ’ya’yan nawa. Wannan shi ne mafarin komai a cikin kasuwar. Sun yi ta ikirarin cewa kasuwar tasu ce da suka kai kara ta zuwa kotu har sau 4 a kan wannan al’amari amma ana korar karar.”

Aminiya ta tambaye shi  game da zarginsa da shugabannin kasuwar ke yi, cewa yana sanya jami’an tsaro suna kama su, sai ya ce: “Ko kusa ba haka ba ne, domin ina so ka sani cewa a matsayina, idan na sa an kama su, ai ba za su sake zama a wannan gari baki daya ba. Ni ban taba kula da abin da suke yi ba, domin tsakaninsu ne da yarana.”

A game da hanyar gyaran wannan al’amari, sai Sarkin Sasa ya ce: “Wannan al’amari ba fada ba ne kuma abu ne mai sauki. Idan suka kyale yarana su shiga kasuwa su yi kasuwanci kamar yadda kowa yake yi, shi ke nan, amma idan suka ki amincewa da hakan, suna neman tayar da hankali ke nan. Idan mutum ya gina gida ya sanya mutane da ’ya’yansa a ciki amma mutanen suka kori yaran daga cikin gidan, za ka amince da haka? Wannan shi ne ainihin abin da ke faruwa a wannan kasuwa. Idan suna so a gyara komai, to wajibi ne su kyale yaran nawa a rika gudanar da harkokin kasuwar tare da su. Ina so ka gane cewa, dukkan masu tayar da kayar baya a kan al’amarin dillalai ne ba fatake  baba.”