✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

 Ana rokon ’yan sanda su dawo aiki a Legas

Bayan kare zanga-zangar #EndSARS an bukaci 'yan sanda su koma bakin aikinsu a jihohin Legas da Ogun.

Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan Sanda, AIG Ahmed Iliyasu mai kuma da shiyya ta 2, ya bukaci jami’an da ke karkashin shiyyar Legas da Ogun su koma bakin aikinsu.

Ya bayyana haka ne a taron kara wa juna sani da aka yi a Onikan, Jihar Legas, inda ya ce ana bukatar cikakken tsaro kafin da kuma bayan bikin Kirsimeti.

“Dole sai mun sauya dabi’unmu wajen kare mutane ya zama shi ne jigon aikinmu”, cewar Iliyasu.

Ya roki jami’an rundunar su mance da abin da ya faru lokacin zanga-zangar #EndSARS su koma bakin aikinsu ba tare da damuwa da yadda matasa ke kallon su ba.

Babban jami’in ya ba wa al’umma tabbacin cewa za a yi gyara a rundunar ta yadda kowa zai iya mu’amala da ita ba tare da tsoro ba.

Sakamakon kurar da zanga-zangar #EndSARS ta bari a baya a Najeriya, ana sa ran samun sauyi daga bangaren hukumar ta ‘yan sandan.