Shugaban Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya ce yana yawan samun sakonnin barazanar kisa.
Abdulrasheed Bawa ya bayyana wa shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels a ranar Talata, cewa ko a makon jiya sai da aka yi barazanar kawar da shi daga ban kasa.
- Sanata Goje ne ya fi dacewa da Shugabancin APC — Kungiyoyin matasa
- ‘Ya kamata a soke hukumomin zaben jihohi’
Da aka tambaye shi game da kalaman da Shugaba Muhammadu Buhari yake yawan furtawa cewa rashawa na ramuwar gayya kan yakar ta da ake yi”, Bawa ya ce. “A makon jiya ina a birnin New York, wani wanda ba a ma binciken sa ya kira wani babba a kasa.
“Matashin ya ce ‘Zan kashe shi (Shugaban EFCCn), zan kashe shi’.
“Ina samun sakonnin barazanar kisa. Don haka gaskiya ne yaki da rashawa yana fuskantar ramuwar gayya,” inji shi.
Game da cin hanci a bangaren aikin gwamnati, Bawa ya ce akwai gibi sosai, musamman a harkar kwangila, kamar “kwangilar yanzu-yanzu”.
“Akwai hukumar gwamnati da ta yi kaurin suna a hakan; Ta mayar da dukkan kwangilolinta a zaman na gaggawa.”
Ya ce EFCC tana da nata dabarun gano nau’ukan cin hanci daban-daban, ciki har da, “Gano yiwuwar cin hanci a kafofi da ma’aikatu.
“Na rubuta wa Ministan kuma nan ba da jimawa ba za mu fara binciken yiwuwar cin hanci a dukkanin ma’aikatu da cibiyoyin gwamnati da ke karkashin Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur domin duba inda suke da nakasu sannan mu ba su shawarwarin abin da ya dace su yi.”
Da aka tambaye shi ko yaki da Najeriya ke yi da cin hancin yana neman ya fi karfinsa, sai ya amsa da cewa “Eh kuma a’a.”