Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara, Mahdi Aliyu Gusau, wanda ake shirye-shiryen tsigewa ya ce ana yi masa makarkashiya ne saboda ya ki sauya sheka da gwamnan jihar, Bello Matawalle zuwa jam’iyyar APC.
Mataimakin Gwamnan, ya ce rashin komawar ce ta sa aka taso shi gaba, kuma hakan ba zai sauya masa ra’ayi ba.
A ranar Litinin ne kwamitin da Babbar Mai Shari’a ta Jihar ta kafa, zai zauna don jin ba’asin Mataimakin Gwamnan, game da wasu tuhume-tuhume da a ke yi a kansa.
Sai dai ya ce ba zai amsa gayyatar da a ka yi masa ba, domin an saba doka wajen bin ka’idar tsige shi, kamar yadda Kundin Tsarin Mulki ya tanada.
Tun bayan sauya shekar Gwamnan Jihar, Bello Matawalle zuwa APC, suka fara takun saka da Mataimakinsa, lamarin da yake barazanar yin sanadin kujerarsa tare da tuhumarsa kan wata badakalar kudade da suka yi batan-dabo a Jihar.