Girgizar kasa mai karfin maki 5.3 a aka yi a safiyar Talata a yankunan da ke kan iyakar Rwanda da Congo ta kai haifar da fargabar fuskantar sabon aman wuta bayan na ranar Asabar da ya hallaka mutum 32.
A ranar Asabar tsaunin Nyiragongo da ke Jamhuriyar Dimokoradiyyar Congo, wanda kuma daya ne daga cikin tsaunuka masu aman wuta mafiya hadari a duniya, ya yi feshin aman wuta zuwa cikin garin Goma, mai yawan al’umma miliyan biyu.
Tun daga lokacin ake ta samun motsin kasa a yankin sannan tsagin da suka bayyana kan tsaunin da wutar ta bubbugo sun toshe.
Hakan ya haddasa fargabar yiwuwar samun aman wutar karo na biyu, kamar yadda Hukumar Gudun Hijira ta MDD ta bayyana.
Girgizar ta ruguje gine-gine da dama a garin na Goma, amma babu tabbacin ko an samu hasarar rayuka.
Girgizar ta faro ne da misalin karfe 09:03 agogon GMT daga yankin Rugerero a Yammacin Rwanda, a cewar wata jaridar kasar.
Tun ranar Litinin aka fara ganin kasa tana tsatstsage a Goma.
Harkokin kasuwanci sun bude a birnin sannan rayuwa ta koma kamar da ga wadanda ba su rasa muhallansu ba.
Kimanin gidaje dubu guda ne suka ruguje sannan fiye da mutum dubu biyar aman wutar ta raba su da muhallansu, inji Majalisar Dinkin Duniya.