Karancin man fetur ya haddasa dogayen layuka a gidajen sayar da man fetur da ke birnin Landan, inda masu ababen hawa suka shiga cikin kunci.
Kusan makonni biyu kenan ana samun dogayen layuka a gidajen mai a Birtaniya, kuma rahotanni sun bayyana cewar gidajen mai 5,500 daga cikin 8,000 ba su da man kwata-kwata.
- Najeriya A Yau: Shekara 61 Da Mulkin Kai: Gaba Najeriya Take Yi Ko Baya?.
- Dan Majalisa na cikin masu daukar nauyin IPOB —Buhari
Wasu titunan a Landan sun zama kufai ba kowa sai masu babura ne ke yawon neman man fetur a gidajen mai, inda kuma wasu ke sayar da man a jarkoki tamkar yadda ‘yan bumburutu ke yi a Najeriya, idan aka shiga karancin man fetur.
Gwamnatin Birtaniya da dillalan da ke dakon man fetur a kasar sun bayyanna cewar, kasar na da isasshen man fetur amma ba ta da isassun motocin da za su yi dakon man zuwa gidajen mai.
Rahotanni sun bayyana cin mutuncin direbobin da ke dakon man na daga cikin abin da ya jawo karancin man a fadin kasar.
Kazalika, matsalar man ta jawo wa tattalin kasar koma baya, inda darajar kudin kasar na ‘Sterling’ ke ci gaba da faduwa a ‘yan kwanakin nan.
Har wa yau, hakan ya sanya fargaba a zukatan wasu inda suke ganin lamarin ka iya jawo karin farashin man fetur din.
Sai dai shugaban kungiyar masu dakon man fetur na kasar (PRA), Brian Madderson ya gargadi gwamnatin kasar kan kara farashin man.
Wasu bayanain sun ce duk da matakin hukumomi na tura rukunin wasu tankoki na ko-ta-baci don kai man fetur a yammacin ranar Laraba, har yanzu lamarin bai inganta ba.
Sakataren harkokin kasuwanci Kwasi Kwarteng ya ce fararen hula ne ke tuka tankokin man daga defo-defonsu a Cambridgeshire da West Yorkshire.
Ya kuma ce sojoji za su fara aikin safarar man a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.
Don ganin wannan matsala ta kau, Firanminista Boris Johnson ya ce gwamnatinsa za ta ba da biza ga direbobin tankokin mai 5,000 daga kasashen waje don su yi aikin dakon mai a kasar.