✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana ci gaba da tsare tsohon jami’in ’yan sanda kan tuhumar fyade

Wata kotu a Kalaba Jihar Kuros Riba ta bayar da umarni a ci gaba da tsare mai mukamin  mataimakin Sufuritanda  ’yan sanda mai murabus DSP…

Wata kotu a Kalaba Jihar Kuros Riba ta bayar da umarni a ci gaba da tsare mai mukamin  mataimakin Sufuritanda  ’yan sanda mai murabus DSP   Christopher Archibong, da take yin shari’arsa bisa zargin yi wa wata karamar yarinya ’yar shekara tara da haihuwa fyade.

da yake yi wa Aminiya karin haske game da wanda ake tuhuma wani lauya mai suna Barista James Ibor ya shaida wa Aminiay cewa alkalin kotun Ochinke ne ya bayar da umarnin aci gaba da tsare wanda ake tuhuma, har sai nan da wani lokaci domin hakan ya dada ba kotu damar ci gaba da bincikenta a  natse . 

Ibor lauyan da ya gabatar da mai laifin a kotu ya ce: “Babu irin yadda bai yi saddabaru ta hanyar amfani da kudi ko ta neman alfarmar ganin an kori karar ko kuma a saki wanda ake kara, amma ba a samu nasara ba.”

Lauyan ya ce kotu ta bayar da umarni a kai fayil din wanda ake tuhuma sashen binciken wadanda suka aikata  miyagun laifuka,wato DPP. don haka za a ci gaba da tsare mai laifin har tsawon lokacin da dPP suka gama bincikensu .

Christopher Archibong dai ya aikata fyaden ne ranar 31 ga watan Mayun wannna shekara sanadin rauni da yarinyar ta yi ta kasa daure ciwon da ke jikinta, ita kuma ta sanar wa mahaifiyarta daga nan suka dauki mataki sanar da hukuma, inda aka kama wanda ake zargi da aikata fyaden.