✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana ci gaba da ba hammata iska tsakanin Indiya da Pakistan

Jiragen yakin Indiya da Pakistan na na kai wa juna hari ta sararin samaniyar Kashmir, a wani sabon rikici da ke neman kazanta a tsakanin…

Jiragen yakin Indiya da Pakistan na na kai wa juna hari ta sararin samaniyar Kashmir, a wani sabon rikici da ke neman kazanta a tsakanin kasashen biyu.

Gwamnatin Pakistan ta ce ta kai hare-hare ta sama a matsayin martani kan makwabciyarta, ta kuma harbo jiragen saman Indiya biyu da kuma kama matuka jirgen.

Sai dai Indiya ta ce jirginta daya kawai aka kakkabo, kuma ita ma ta harbo wani jirgin Pakistan mai saukar ungulu. Kuma ta ce ta murkushe kokarin Pakistan na kai hari a kan sansanin dakarunta.

Firayi Ministan Pakistan, Imran Khan ya yi gargadi kan halin da wannan rikici ka iya jefa bangarorin biyu inda ya bukaci a shiga tattaunawa da juna.

Tun bayan samun ’yancin kansu a 1947, kasashen sun yi fada da juna  sau uku. Biyu daga cikin yakin duk an yi ne a kan Kashmir.