Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya bayyana cewa akwai mutane da ke aiki karkashin kasa domin ganin an sako dan karajin fafutakar kare yankin Yarbawa, Sunday Igboho da ke tsare a birnin Kwatano na kasar jamhuriyar Benin.
Sanwo-Olu ya bayyana haka ne bayan ya kada kuri’a a mazabarsa da ke Ikoyi a zaben kansiloli da shugabanin kananan hukumomi da aka gudanar a jihar a ranar Asabar 24 ga Yuli, 2021.
- Bayan karbar kudin fansa, ’yan bindiga sun ki sako Daliban Tegina
- ’Yan bindiga sun yi awon gaba da takardun jarabawar NECO a Kaduna
Bayan ’yan jarida sun tambaye shi game da kan shirun da gwamnonin Jihohin Kudu Maso Yamma suka yi a kan tsare Sunday Igboho, sai gwamnan ya ce akwai mutane da ke aiki a karkashin kasa domin a sako shi.
“Muna cikin mawuyacin hali baki daya, amma mutane na aiki a karkashin kasa, ba tu ne da ba ya bukatar a fito a bayyana,” inji shi.
A ranar Litinin ne jami’an tsaro a birnin Kwatano na kasar Jamhuriyar Benin suka tsare Igboho tare da matarsa a lokacin da suke kokarin ketarewa zuwa Turai daga kasar ta Benin.
Gwamnatin kasar ta gurfanar Sunday Igboho da matar tasa a gaban kuliya a ranar Alhamis inda kotun ta ba da belin matar, shi kuma ta ba da umarnin ci gaba da tsare shi har zuwa lokacin da zai sake gurfana a gabanta a ranar Litinin 26 ga Yuli, 2021.