Kotu ta ƙwace wasu kwantainoni 54 mallakin tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele.
Kotu ta ƙwace kwantainonin ne bayan Hukumar Yaƙi da Masu Karya Tattalin Arziƙin Ƙasa (EFCC) ta gano su a wani katafaren dakin ajiyar kaya a Jihar Ogun.
Hukumar EFCC ta gano kwantainonin maƙare da kekunan ɗinki iri-iri ne a ci gaba da binciken da take yi kan zargin Emefiele da karkatar da biliyoyin Naira a lokacin da yake Gwamnan CBN.
Bayan gano kwantainonin EFCC ta ba samu umarnin kotu na wallafa bayanansu a jaridun idan da mai su ya yi bayani.
Daga bisani bayan cikar wa’adin ba tare wani ya yi ikirarin mallakar kayan ba, kotun ta mallaka wa gwamnati kadarorin.
Wakikinmu ya yi kokarin samun ƙarin bayani daga kakakin Hukumar EFCC, Wilsom Uwujaren, amma hakan bai yiwu ba.
Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan EFCC ta gano wasu gidadje sama da 750 a wani rukunin gidaje a Abuja.
EFCC ba ta bayyana mai gidajen ba, amma wasu majiyoyi sun da danganta su da Emefiele.