Rahotanni na cewa wasu mutum uku sun baƙunci lahira bayan zartar musu da hukuncin kisa sakamakon kama su da laifin fyaɗe a ƙasar Iran.
Kamfanin labarai na Mizan mai alaƙa da ma’aikatar shari’a ya ruwaito cewa an aiwatar da hukuncin ne da tsakar daren Asabar da ya gabata a wani gidan yari da ke birnin Gorgan.
- Abin da ya hana Ganduje zuwa tarbar Tinubu a Kano
- Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 9 a hanyar Maiduguri-Damaturu
Shugaban sashen shari’a na lardin, Heidar Asiabi, ya ce an fara bincike ne bayan wata mace ta shigar da ƙorafin yin garkuwa da ita.
A cewarsa, bayan tsananta bincike ne kuma wasu matan uku suka fito da bayanai da ke tabbatar da zargin aikata fyaɗe.
“Saboda girma da kuma kamanceceniya wajen aikata laifin aka kafa wata tawaga ta musamman da ta ƙunshi alƙalai da jami’an tsaro,” in ji Asiabi.
Bayan gano gungun mutum ukun cikin gaggawa, an kai su kotu tare da yanke musu hukunci, inda ita ma kotun ƙoli ta amince da shi.
Galibi dai ana aiwatar da hukuncin kisan ne a gidajen yari, amma a farkon wannan watan a yankin Arewa maso Yamma an zartar wa wani mutum hukuncin rataya a bainar jama’a wanda aka samu da laifin kisan wata yarinya bayan ya yi mata fyaɗe.
Iran ta zartar wa aƙalla mutum 901 hukuncin kisa a 2024 kaɗai, a cewar Volker Turk, shugaban hukumar kare haƙƙi ta Majalisar Ɗinkin Duniya.