An zargi wani jami’in soja da azabtar da wani yaro mai kimanin shekara 10 da haihuwa har sai da ya mutu saboda tsinkar mangwaro a barikin sojoji.
Ana dai zargin yaron ne wanda mazaunin unguwar Hayin Banki ne a Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa da zuwa shan mangoron a barikin sojoji.
- Kotu ta dakatar da shirya mukabala tsakanin Abduljabbar da malaman Kano
- ‘Mun kama soja dumu-dumu yana ba ’yan ta’adda kaki da albarusai’
Aminiya ta gano cewa marigayin ya shiga barikin Kotoko ne da ke a
unguwarsu da nufin shan mangoron, ko da yake babu cikakken bayanin ko shi kadai ya je ko kuma tare da abokansa ba.
Sai dai rahotanni sun ce sojan ya bi yaron har zuwa cikin unguwarsu inda ya kamo shi ya kai shi cikin barikin ya azabtar da shi.
Wani mazaunin yankin kuma Sardaunan Hayin Banki, Malam Ibrahim Hassan Wuyo ya ce yaron ya shiga barikin na Kotoko ne da nufin tsinkar mangaro, amman sai sojan ya nemi jin dalilin da ya sa ya shigo barikin, inda shi kuma ya yi kokarin guduwa.
A cewar Sardaunan, “Daga nan ne sojan ya bi sahunsa har cikin unguwarsu, ya kamo shi ya mayar da shi cikin barikin inda ya rufe shi.
“Na sami labarin cewa a lokacin da yake azabtar da yaron sauran abokan aikinsa sojoji sun nemi ya kyale shi amma ya ki,” inji shi.
A cewar Sardauna, wahalar da yaron ya sha ce ta yi sanadiyyar rasuwarsa, kafin daga bisani sojan ya je ya jefar da gawarsa a unguwar Kanawa.
Tuni dai Rundunar Sojoji ta mika wanda ake zargin ga hukamar ‘yan sanda domin su fadada bincike a kai.
Kakakin Rundanar ‘Yan Sandan jihar ta Kaduna, ASP Mohammed Jalige ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce tuni an fara bincike a kai.
Sai dai Aminiya ta gano cewa har yanzu gawar yaron na hannun hukumar ‘yan sanda.