✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An zargi miji da dukan matarsa har sai da ta ce ga garinku nan

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Legas ta fara gudanar da bincike kan wani mutum mai shekaru 42 da ake zargi da lakadawa matarsa duka har sai…

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Legas ta fara gudanar da bincike kan wani mutum mai shekaru 42 da ake zargi da lakadawa matarsa duka har sai da ta ce ga garinku nan.

Lamarin dai ya faru  ne a gidan ma’auratan da ke layin Joado a unguwar Oke Ira Nla, Ajah a birnin Legas.

Rahotanni sun ce tunda farko dai musu da hatsaniya ne suka kaure tsakaninta ma’auratan kan zamantakewarsu ta aure, inda ya rufe da duka har ya ji mata ciwo.

Lamarin dai ya faru ne ranar 16 ga watan Febarairun 2021 da misalin karfe 10 na dare.

Sai dai mijin ya musanta zubarwa da matar tasa jini da kuma gaza kai mata dauki lokacin da take cikin galabaita.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar, CSP Adejobi Olumuyiwa ya tabbatar da faruwar lamarin.

Adejobi ya kara da cewa ofishin ‘yan sanda na yankin Langbasa ne ke kula da lamarin.

Ya ce sun sami labarin lamarin ne ta korafi da suka samu daga makwabcin ma’auratan.

Ya ce tuni aka cafke mutumin da ake zargi da aikata kisan kuma za su gurfanar da shi gaban kuliya don ya girbi abinda ya shuka.