✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An zargi dillalan fetur da zagon kasa a Ondo

Wani dan kasuwa a garin Ore cikin Jihar Ondo, Alhaji Ibrahim Autan Gayu ya dora laifin karancin fetur ga dillalai da ke wa Shugaba Muhammadu…

Wani dan kasuwa a garin Ore cikin Jihar Ondo, Alhaji Ibrahim Autan Gayu ya dora laifin karancin fetur ga dillalai da ke wa Shugaba Muhammadu Buhari zagon kasa.

dan kasuwar ya ce, “wasu ’yan siyasa ne tare da miyagun mutane marasa kishin kasar haihuwarsu suka kulla wannan makirci da suka kirkiri hanyoyin boye man fetur domin shafa wa Gwamnatin Buhari kashin kaji.”

Ya fadi haka ne cikin zantawa da Aminiya, inda ya ce, “rashin kishin kasa ne ya sa muke cutar kanmu da kanmu da jefa jama’a cikin halin damuwa saboda mummunan burinsu. Ya kamata Shugaba Buhari a matsayinsa na Ministan man fetur ya hanzarta kafa kwamitin gaggawa da zai binciki wannan muhimmin al’amari domin gano ainihin masu yin zagon kasa a kan wannan matsala ta karancin mai a Najeriya. Kuma a yi masu hukunci daidai da irin laifin cin amanar kasa da suka yi.”

Da yake amsa wata tambaya,  ya yi watsi da jita-jitar irin wadannan mutane cewa, ba a samun matsalar karancin man fetur a lokutan bukukuwan Musulmi na Sallah sai a lokacin bikin Kirista. Ya ce, irin wadannan kalamai ne na tunzura jama’a da ya kamata a yi hukumci mai tsanani ga masu yayata su.

Dangane da tsadar kayan masarufi a dalilin karancin man fetur kuwa sai ya ce, “an samu karin farashin abubuwan bukatun yau da kullum ne a cikin makonni 3 da suka gabata, a dalilin tsadar abubuwan hawa na dakon kaya daga birane zuwa sauran garuruwa. Amma abun farin ciki musamman a nan Jihar Ondo, karuwar farashin irin wadannan kaya ba su tsawwala ba saboda jama’a sun gane gaskiyar cewa wasu mutane ne suke yin amfani da wannan dama wajen haifar da tsadar rayuwa ga ’yan uwansu.”