✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi zanga-zanga kan hana amfani da takardun kudi a Indiya

dimbin mutane ne suka fito zanga-zanga a manyan biranen kasar Indiya da dama, domin nuna adawa da matakin gwamnati na haramta amfani da manyan takardun…

dimbin mutane ne suka fito zanga-zanga a manyan biranen kasar Indiya da dama, domin nuna adawa da matakin gwamnati na haramta amfani da manyan takardun kudi biyu na kasar.
A farkon wannan watan ne gwamnati ta sanar da haramta amfani da takardun kudin Rupee na 500 da 1,000, al’amarin da ya haddasa rudani yayin da mutane suka rika jan dogayen layuka a bankuna don sauya tsofaffin kudinu, kamar yadda kafar yada labarai na BBC ya bayyana.
Firaminista kasar Narendra Modi ya kare matakin da cewa hakan zai rage matsalar cin hanci a kasar.
Amma jam’iyun adawa sun soko matakin. A makon jiya ne suka dakatar da duk wasu harkoki a majalisar dokoki, kana suka bukaci Mista Modi ya nemi afuwa kan daukar wannan mataki.
Masu aiko da rahotanni sun ce babu tabbaci kan yawan mutanen da za su fita zanga-zangar, yayin da ’yan kasar  da dama ne suka goyi bayan matakin, duk da cikas din da hakan ya haifar musu.