✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi zanga-zanga kan hana amfani da takardun kudi a Indiya 1

Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce gwamnatin tarayya  ta kasha Dala biliyan daya (kimanin Naira biliyan 400) a shekarar 2015 wajen tallafin kananzir a…

Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce gwamnatin tarayya  ta kasha Dala biliyan daya (kimanin Naira biliyan 400) a shekarar 2015 wajen tallafin kananzir a kasar nan.
Kodayake, gwamnati ta dakatar da biyan tallafin kananzir a watan Mayun shekarar 2016, Osinbajo ya ce tsarin ya haifar da babbar asara ga kasar nan musamman ta fuskar kudin kasashen ketare.
Mataimakin Shugaban kasar yayin wani taro na masu ruwa da tsaki kan makashi, ya ce gwamnatin tarayya tana wani shirin na wadata jama’a da iskar gas don fara amfani da ita wurin girki.
“Kashi 40 cikin 100 na girki da iskar gas din da aka yi amfani da ita  shekarar 2015 a kasar nan, an shiga da ita ne daga kasashen ketare,” inji shi. Ya ce gwamnati ta fara daukar matakai don ganingalibin jama’ar kasar nan fara amfani da iskar gas a matsayin makamashi.
Ya ce nan da shekara 15 masu zuwa, gwamnati ta shirya wadata gidaje miliyan 21 da iskar gas a matsayin makamashi.
Farfesa Osinbajo ya ce saboda karancin iskar gas ne ya sa galibin jama’ar kasar suke amfani da itace wajen girki, wanda hakan yake gurbata muhalli. Kuma ya haifar da cututtuka.