✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi watsi da karar da Liberpool ta yi kan Sadio Mane

A ranar Talatar da ta wuce ne Hukumar shirya kwallon kafa ta Ingila (FA) ta yi watsi da karar da kulob din Liberpool ya yi…

A ranar Talatar da ta wuce ne Hukumar shirya kwallon kafa ta Ingila (FA) ta yi watsi da karar da kulob din Liberpool ya yi a kan dan dagewar da aka yi wa dan kwallon gabanta Sadio Mane.

Tun da farko, kulob din ya daukaka kara ne bayan hukumar ta dage dan kwallon daga yin wasanni uku bayan an ba shi jan kati saboda tokarin da ya yi wa golan Manchester City a wasan da suka yi ranar Asabar da ta wuce.  A wasan, Manchester City ce ta lallasa Liberpool da ci 5-0 kuma jan katin da aka ba Mane ya taimaka wa City wajen samun galaba a kan kulob din Liberpool a wasan.

Kulob din Liberpool dai ya daukaka kara ne a kan dagewar da Hukumar ta yi wa Mane daga yin wasanni uku.

A daidai minti na 37 ne Mane ya samu katin kora bayan ya tokari golan Manchester City, inda nan take alkalin wasan ya ba shi katin kora.

Bayan wasan ne  Hukumar FA ta Ingila ta yi nazari a kan wasan kuma ta dage shi daga yin wasanni uku saboda laifin da ya aikata.

Yanzu dan kwallon ba zai buga wasan Liberppol da na Burnely a gobe Asabar ba da kuma wasan da kulob din zai yi da na Leicester City a makon gobe da kuma wani wasa a gasar cin kofin League Cup na Ingila.