✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi wa ’yan kwallon Chelsea kyautar agogon Naira miliyan 14 kowannensu

Dan kwallon Najeriya Bictor Moses da yanzu haka yake buga wa kulob din Chelsea na Ingila kwallo yana daga cikin  wadanda mai kulob din Chelsea…

Dan kwallon Najeriya Bictor Moses da yanzu haka yake buga wa kulob din Chelsea na Ingila kwallo yana daga cikin  wadanda mai kulob din Chelsea Roman Abramobic ya yi musu kyautar agogo da aka kiyasta kudinsa a kan Fam dubu 30 kwatankwacin Naira miliyan 13 da dubu 900.

Mai kulob din ya yi wa ’yan kwallonsa wannan kyauta ne saboda nasarar lashe gasar rukunin firimiyar Ingila da suka yi a kakar wasan da ta wuce ta 2016 zuwa 2017.  Mai kulob din ya ce ya yi musu wannan karamci ne saboda faranta masa ran da suka yi, inda ya yi fatar za su zage damtse don ci gaba da samun nasara a kakr wasa ta bana.

Daya daga cikin ’yan kwallon da suka samu wannan kyauta kuma haifaffen Brazil Willian ne ya fallasa wannan kyauta a shafin sadarwasa na Twitter inda ya sanya hoton agogon da kuma yawan kudin.

In ban da Willian, daukacin ’yan kwallon da suka samu wannan kyauta ba su bayyana wa duniya ba, don haka za a iya cewa tamkar Williamya ya ari bakinsu ne kuma ya ci musu albasa.

Bictor Moses, dan shekara 26, yana daga cikin ’yan wasan Super Eagles, ya yi wa Chelsea wasa sau 34 a kakar wasan da ta wuce inda ya samu nasarar zura kwallaye uku a ragar  Burnley da Leicester City da kuma na Tottenham a gasar firimiyar Ingila.