✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi wa shirin ruga mummunar fahimta –  Sarkin Fulanin Legas

Sarkin Fulanin Jihar Legas Alhaji Muhammadu Bambado, ya ce mutanen da suka yi ta karaji suna sukar shirin ruga da Gwamnatin Tarayya ta yi yunkurin…

Sarkin Fulanin Jihar Legas Alhaji Muhammadu Bambado, ya ce mutanen da suka yi ta karaji suna sukar shirin ruga da Gwamnatin Tarayya ta yi yunkurin assasawa sun yi wa shirin mummunar fahimta. Ya  ce da sun san alfanun shirin ga al’umma da kasa baki daya ba za su fito suna cece -ku-ce ba.

Sarkin Fulanin ya shaidawa Aminiya cewa, abin takaici ne yadda wadansu batagari ke amfani da kafafen sada zumunta na zamani wajen yada labaran karya tare da rura gaba da kiyayya a tsakanin kabilun kasar nan kan shirin na Ruga da Gwamnatin Tarayya ta yi yunkurin yi. “Da farko wadansu batagari sun yi ta shiga kafafan sadarwar zamani suna yada bayanan karya da farfaganda domin kushe shirin. Ni kaina sai da aka ta yada labaran karya game da ni, wai an mayar da ni babban Sarkin Legas wato ‘Emir of Lagos’. Sannan wata kafar ta rubuta labarin wai Gwamnan Legas ya kawo ziyara fadata, duk sun yi haka ne domin a harzuka jama’ar wannan yanki game da sha’anin ruga, domin wannan hoto da aka yi ta yayatawa wai Gwamna ya ziyarce ni, ba hoto ne da aka dauka yanzu ba, an dauke shi ne lokacin da Gwamnan Legas yake yakin neman zabe inda ya ziyarci fadata domin neman goyon bayanmu, kuma a ranar da kafar ta ce Gwamnan ya ziyarce ni ba na Legas na tafi Abuja, sai ranar Talatar da ta gabata na dawo,” inji shi.

Ya ce, mutane sun yi wa shirin ruga mummunan fahimta, maimakon su tsaya su fahimci manufar gwamnati na bullo da shirin, “Mutumin da bai fahimci abu ba yaya za a yi ya san amfaninsa ko akasin haka? Wannan shiri ne da in har aka yi zai kawo karshen rikicin Fulani makiyaya da manoma, kuma abu mafi mahimmaci shi ne a bai wa ’ya’yan Fulani makiyaya ilimi, ilimi shi ne mabudi, ilimtar da ’ya’yan Fulani makiyaya shi ne kashin bayan magance rikicin da ake alakanta su da shi,” inji shi.