✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi wa makiyaya 12 bulala saboda shiga gonakin manoma a Adamawa

Makiyaya 12 ne aka yi wa bulala sakamakon shiga da dabbobinsu cikin gonakin manoma a Unguwar Bola da ke Karamar Hukumar Yola ta Kudu a…

Makiyaya 12 ne aka yi wa bulala sakamakon shiga da dabbobinsu cikin gonakin manoma a Unguwar Bola da ke Karamar Hukumar Yola ta Kudu a Jihar Adamawa bayan an yi yarjejeniyar zaman lafiya a tsakanin makiyaya da manoma.

Domin yin sulhu a tsakanin makiyaya da manoma a jihar, an yi wata yarjejeniyar cewa duk manomin da ya ga dabba a gonarsa ba zai kashe ba sannan makiyayan za su biya adadin barnar da dabbarsu ta yi a gonakin makiyaya tare da yi wa duk wanda aka kama dabbarsa tana barna a cikin gonakin manoma bulala.

Shugaban Tabital Pulaku, Alhaji Ya’u ne ya bayyana haka lokacin da ake bikin yarjejeniyar sulhu a tsakanin makiyayan da manoma inda ya bayyana cewa an hana yara kanana kiwo sannan duk wanda aka kama dabbobinsa a gonakin manoma za a yi masa bulala tare da sanya shi biyan kudin barnar.

Ya ce sun hana kiwon dare sannan ya ja kunen iyaye su kula da inda ’ya’yansu suke idan dare ya yi domin dakatar da harkokin shaye-shaye a tsakanin matasa.

Shugaban Kungiyar Murmushi Debelopment Foundation, Babagari Baraya wanda shi ne ya nemo tsarin yin sulhun a tsakanin makiyaya da manoman ya ce sun yi haka ne domin a samu zaman lafiya.

Ya ce sun saurari koke-koken jama’a game da asarar da suke samu bayan sun yi shuka hakan ne ya sanya suka nemo mafita domin dakatar da irin wannan barnar dukiya.

Ya ce Ofishin Jakadancin Birtaniyya ya dauki nauyin wannan sulhu domin samar da zaman lafiya a tsakanin makiyaya da manoma.

Mai Jimillan Yola, Alhaji Mohammed Mustafa ya nuna farin cikinsa game da irin wannan tsari na neman mafita a tsakanin makiyaya da manoma a Jihar Adamawa baki daya.