Mahukunta a Tanzaniya sun sanar da karin albashi ga ma’aikatan gwamnati, matakin da ake gani zai rage wa al’umma radadin tsadar rayuwa da ake ciki.
Shugabar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan ta amince da karin mafi karancin albashi da kaso 25 cikin dari, wannan karin na zuwa ne a daidai lokacin da al’ummar kasar ke fama da matsin tattalin arziki.
- Tsohon dan wasan Barcelona, Maxi Rolon ya mutu a hatsarin mota
- Harin ‘Yan bindiga: Mazauna karkara sun gudu birni neman mafaka a Neja
Ko baya ga wannan karin, Shugaba Samia ta sanar da kara albashin ma’aikatan gwamnati, wanda ke zama karon farko tun daga shekarar 2016 kamar yadda Gidan Rediyon Jamus ya ruwaito.
Tun bayan darewa karagar mulki a shekarar da ta gabata bayan mutuwar Shugaba John Magufuli, sannu a hankali shugabar Tanzaniyar kuma mace ta farko kan wannan mukami, ta fara sauya akalar gudanarwar gwamnatin marigayin.