✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi wa Kwamishina kisan gilla a Katsina

Mahara sun daba mishi wuka a gidansa bayan Sallar La'asar ranar Alhamis

Wasu da ba a san ko su wane ne ba sun yi wa Kwamishinan Kimiyya da Fasaha na Jihar Katsina, Dokta Rabe Nasir, kisan gilla.

Maharan sun daba wa kwamishinan wuka ne a gidansa da ke Rukunin Gidajen Fatima Shema a garin Katsina a yammacin ranar Alhamis.

Majiyarmu ta ce,  “An daba wa marigayi Dokta Rabe Nasir wuka ne bayan Sallar La’asar a gidansa da ke Rukunin Gidajen Fatima Shema.”

Kafin zamansa kwamishina, marigayi Dokta Rabe shi ne Mashawarcin Gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina a kan Kimiyya da Fasaha.

Dokta Rabe Nasir haifaffen garin Mani ne a Karamar Hukumar Mani ta Jihar Katsina kuma an haife shi ne a watan Oktoban 1960.