✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi wa Fursunonin Najeriya karin kudin abinci

Kudin abincin fursunonin ya tashi daga 450 inda ya koma 750.

Kwamitin Majalisar Dattawa kan harkokin cikin gida ya soma wani yunkuri na kara wa fursunonin da ke gidajen yarin Najeriya kudin abinci.

Batun ya taso ne ranar Laraba lokacin da shugaban gidajen yarin Najeriya, Haliru Nababa, ya je gaban kwamitin domin kare kasafin kudin hukumar na 2022.

A cewar kwamitin, akwai fursunoni 66,340 a gidajen yari da ke fadin Najeriya, kuma a cikinsu har yanzu ba a yanke wa fursunoni 47,559 hukunci ba.

Daga nan kuma Sanata Utazi, ya bayar da shawara a madadin kwamitin cewa ya kamata a rika ba kowanne fursuna N750 domin sayen abinci.

A nasa martanin, shugaban hukumar kula da gidajen yarin, ya ce an kara kudin kashewar fursunonin daga N450 zuwa N750 a kowacce rana a cikin kasafin kudin 2022.

Wannan na zuwa ne bayan kiraye-kirayen da aka sha yi kan karin kudin abincin da fursunonin ke ci, duba da yadda al’amura ke sauyawa.