Gwamnatin Nasarawa ta ce ta kammala shirin raba tallafin karatu na miliyan N218, ga dalibai 8,000 ’yan asalin jihar da ke karatu a manyan makarantun a ciki da wajen jihar.
Babbar Sakatariyar Hukumar Bayar da Tallafin Karatun, Hajiya Sa’adatu Yahya, ta ce tuni gwamnan jihar, Abdullahi Sule ya amince da fitar da fiye da miliyan N100 domin fara biya.
Ta ce za ayi rabon ne kashi biyu, kuma za a fara ranar 4 ga watan Nuwamba, a cibiyoyi daban-daban na jihar, kuma, “Da an kammala kashin farko na rabon ranar 4-ga wata.
“Kuma da zarar an mika wa gwamna duk takardun da suka kamata, za a fara biyan kashi na biyu.
“Ina kuma farin cikin sanar da daliban cewa sakamakon matsin tattalin arziki da ake fama da shi, an kara yawan kudin tallafin.
“Dalibai masu nazarin aikin lauya za su samu N300,000 madadin N100,000 da suka saba karba.
“Sai sauran daliban da ke karatun digirinsu na farko da za su karbi N20,000 madadin 10,000.
“Masu bukata ta musamman kuma za su karbi N30,000, a madadin N20,000.”
Ta kuma ce duk wannan karin da aka yi wa sauran bangarori da ke karatun Digiri na farko, zai fara aiki ne a wannan biyan, illa na masu nazarin aikin Lauya.
Jami’ar ta bayyana cewa dalili shi ne, sai bayan an saki kudin sannan aka amince da biyan su sabon tsarin.
Ta kuma ce za a fara tantance daliban da za su ci gajiyar daga karfe 9:00 na safe, zuwa 3:30 na yamma kullum, a sakatariyar mazabar Nasarawa ta Arewa, daga ranar 20-24, ga Oktoba.
Sai kuma ranar 25 zuwa 27 da za ayi a Nasarawa ta Yamma, yayin da a ta Kudu kuma za a yi ranar 31 ga watan Oktoba zuwa 4 ga wata.