✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi wa almajirai 1,000 rajistar inshorar lafiya a Gombe

Za a riƙa duba lafiyar daliban makarantun Tsangayar kyauta a ƙarƙashin shirin inshorar lafiyar jihar

Gwamnatin Gombe ta yi wa daliban makarantun tsangaya fiye da 1,000 rajista domin duba lafiyarsu kyauta a ƙarƙashin shirin inshorar lafiya ta jihar.

An yi wa almajiran rajista ne a wani ɓangare na samar da isasshen kiwon lafiya ga ƙananan yara masu ƙaramin ƙarfi a jihar.

Da yake ƙaddamar da shirin, wanda ofishin Mashawarcin Gwamna kan Makarantun Tsangaya, ya shirya, Mataimakin Gwamnan, Dokta Manassah Jatau ya jaddada aniyar Gwamnatin na inganta kuka da lafiyar ƙananan yara da masu ƙaramin karfi.

Ya ce nan gaba jihar za ta ƙaddamar da tsarin kula da lafiya na tafi-da-gidanka mai suna GoHealth domin waɗanda ba su da ƙarfin zuwa asibiti su samu sauƙi.

“Idan babu irin waɗannan tsare-tsare mutane da yawa ba za su iya kula da lafiyarsu ba, saboda su masu ƙaramin ƙarfi ne.

“Shi ya sa a yau muka ƙaddamar da yin rajistar almajirai 1,000 a ƙarƙashin shirin inshorar lafiya na jihar Gombe.”

Dr. Jatau ya bayyana kasancewar almajirai ƙananan yara masu ƙaramin ƙarfi da kuma yadda suke fuskantar barazanar kamuwa da ƙwayoyin cuta ya sa shirin ya ka ba su muhimmanci.