✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi wa alkali dungu wajen kwace kadarorina – Saraki

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Abubakar Bukola Saraki, ya ce ba a gabatar wa alkalin Babbar Kotun Tarayya ta Ikoyi cikakken bayanin gaskiya ba game…

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Abubakar Bukola Saraki, ya ce ba a gabatar wa alkalin Babbar Kotun Tarayya ta Ikoyi cikakken bayanin gaskiya ba game da kadarorinsa da kotu ta kwace na wucin-gadi ba.

Sanata Saraki ya ce tabbas ba a sanar da kotun komai game da wani umarni da wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar ba, inda ta hana Hukumar EFCC daukar wani mataki kan kwace wadannan kadarori da ake magana a kansu ba, har sai ta yanke hukunci kan wata kara da ke gabanta.

Lauya Nnaemeka Omewa na Hukumar EFCC ne ya gabatar da bukatar a kwace wadannan kadarori a gaban Mai shari’a Mohammed Liman wanda ya amince tare da bayar da umarnin kwace kadarorin biyu a matakin wucin-gadi.

Shugaban Sashin Hulda da Jama’a na Hukumar EFCC, Wilson Uwujarem ya tabbatar wa manema labarai wannan hukunci na kotun Legas.

Hukumar EFCC ta ce ta shaida wa kotun cewa tsohon Shugaban Majalisar Dattawan ya mallaki kadarorin biyu ne ba ta hanyar halal ba, lokacin da yake Gwamnan Jihar Kwara. Hukumar ta zargi Saraki da fitar da Naira biliyan 12 daga asusun jihar ya kuma shigar da su cikin asusun ajiyar daya daga cikin mataimakansa na musamman, Abdul Adama a lokuta daban-daban.

Sai dai a martanin da ya mayar Bukola Saraki ya ce ya yi imani ba a sanar da kotun cewa kadarorin da ake magana a kansu, kotu ta riga ta yanke hukunci a kansu tun a ranar 6 ga Yulin bara ba. Ya ce Kotun Koli ta ayyana cewa hanyar da aka samu kudin sayen ba ta haram ba ce kamar yadda masu gabatar da kara suka yi ikirari.

Hukumar EFCC ta ce kadarorin sun kunshi gini mai lamba 17A a titin McDonald da ke Ikoyi, Legas wanda ake zargin an saye su ne da dukiyar da aka samu ta haramtatciyar hanya.