✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi taron magance tsadar abinci a Filato

Kungiyar Dilolin Amfanin Gona ta Najeriya (NAAPD) reshen Jihar Filato ta shirya taron masu ruwa da tsaki don a bunkasa samuwar abinci a Najeriya da…

Kungiyar Dilolin Amfanin Gona ta Najeriya (NAAPD) reshen Jihar Filato ta shirya taron masu ruwa da tsaki don a bunkasa samuwar abinci a Najeriya da kuma samar da sabbin matakai wajen magance biyan haraji ba bisa tsari ba da magance satar amfanin gona a lokacin jigilarsa a kan hanya daga wani gari zuwa wani.

A yayin taron wanda aka gudanar da shi a hedikwatar kungiyar direbobi NURTW da ke Jos a ranar Litinin da ta gabata an bukaci gwamnati ta tashi tsaye wajen samar da hanyoyin rage tsadar abinci a kasar nan.

A cikin waxanda suka halarci tsaron akwai Hukumar ’Yan Sanda ta Najeriya da Kungiyar direbobi ta NURTW da kungiyar Masu Motoci ta NARTO da Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) da Kungiyar Manoma ta Najeriya (AFAN) da Kungiyar Dilolin Ganyayyaki ta Najeriya (BDAN) da kungiyar masu kayan gwari da kungiyar dilolin shinkafa da sauransu.

A lokacin da yake jawabi Kodinetan Kungiyar Dilolin Amfanin Gona na Najeriya, (NAAPD) na Shiyyar Arewa ta Tsakiya, Mista Jonah Ogbaji ya bukaci gwamnatin tarayya ta tashi tsaye wajen ganin an kawo karshen tsadar abinci a kasar nan.

Ya ce, “A yanzu kuxin da mutane suke kashewa kafin a kammala dafa musu abinci har a xora musu a teburin cin abinci ya nunku da kusan kashi 1000, domin manoma kafin su kai ga girbi suna kashe makudan kuxaxe wajen sayen taki da maganin kwari da sauransu

“Sannan bayan sun noma sai batun jigilarsa, inda shi ma ake kashe kuxi sosai, sannan ga harajin da ake biya mara kan gado, inda a wata jiha ma sai waxansu sun biya fiye da biyu, don haka dole abinci ya yi tsada.” Inji shi.

Ya bukaci direbobin da ke jigilar kayan  abinci da kada su kuskura su biya haraji ga waxanda suka same su a kan hanya, idan ba wurin xaukar kayan da kuma saukewa ba, sannan su rika kai motocinsu ga cibiyar bankaxo cutuka don a kai ga magance yaxuwar cutuka da aka samu daga amfanin gona.

Jami’in Kwamitin ’Yan Sanda da ke dakile satar shanu na Shiyyar Arewa ta Tsakiya, Yahaya Usman ya bayyana cewa hukumar ’yan sanda a shirye take wajen haxa kai da kungiyoyin da ke da ruwa da tsaki wajen nomawa da jigila da dillanci da kuma kasuwancin amfanin gona, don ganin an kawo karshen tsadar abinci a kasar nan.

Ya kuma yi alkawarin cewa ’yan sanda za su jajirce wajen ganin sun kama duk wanda yake tsayawa a kan hanya yana karbar haraji a kan kayan amfanin gona ba bisa ka’ida ba.

Shugaban Kungiyar Dilolin Amfanin Gona ta Najeriya (NAAPD) reshen Jihar Filato, Mista Samuel Yusuf Hamman ya koka kan yadda amfani gona ke rubewa sakamakon yadda masu karbar haraji ba bisa ka’ida ba ke yi wa direbobinsu.