✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi taron bunkasa noman shinkafa a Younde

An yi taron masana kan noman shinkafa a birnin Yaounde, inda taron ya hada masu bincike a fannin fasahar noman zamani na sassan duniya,  wadanda…

An yi taron masana kan noman shinkafa a birnin Yaounde, inda taron ya hada masu bincike a fannin fasahar noman zamani na sassan duniya,  wadanda suka yi musayar sani akan karin wasu dabarun da za a rika amfani da su wurin bunkasa noma, domin kasashen Afrika su samu rage dimbin shinkafar da suke shigowa da ita daga ketare.
kasashen Afrika na batar da makudan kudi dangane da haka. Saboda haka aka kiyasta yawan ragin da ake so a yi  akan shinkafa ton miliyan bakwai zuwa shekara ta 2020. Dangane da haka ne taron ya fi mayar da hankali kan bincike, domin manoma su ribaci sababbin dabaru da za su taimaka wajen bunkasa albarkatun nomansu.
A yanzu dai, tarin kasashen Afrika na dogaro ne da hanyar shigowa da shinkafa daga ketare wurin samun isasshen hatsin. Yin Haka a fadar masu bincike, na nuna sabani tsakanin yanayi mai ni’ima  da kuma kasa mai albarka da nahiyar take kunshe da su, wadanda kuma  wata dama ce da manoman shinkafa ka iya ribantuwa da su wurin fadada kadadar da suke yin amfani da ita a harkar noman tasu.
Wata matsalar da ake fama da ita, ita ce na yin noman a gargajiyance. Nahiyar Afrika dai na amfani da ton din shinkafa miliyan 24 wurin ci a kowace shekara. A bara kuma an kashe biliyan 5 na Dalar Amurka wurin cike gibin bukatar da nahiyar ke da ita na samun shinkafa. Ganin hakane ta sanya cibiyar bunkasa noman shinkafa ta Afrika yunkurin rage adadin shinkafa da ake shigowa da ita. Samun cinma wannan manufar kuma zai ba nahiyar damar  isar wa kanta da kanta da kashi kusan 90 cikin 100 da nomar da za ta bunkasa yi karkashin tsarin amfani da sababbin dabaru na zamani.