Wata babbar kotu da ke garin Ado-Ekitia Jihar Ekiti, ta yanke wa wani matashi hukuncin daurin rai da rai kan laifin yi wa ’yar makwabcinsa mai shekara 14 fyade.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa an gurfanar da matashin a gaban Mai Shari’a Monisola Abodunde, tun a ranar 9 ga watan Satumba 2021, kan zargin yi wa yarinyar fyade.
- PDP ta jajanta wa APC kan hatsarin jirgin ruwan magoya bayanta a Delta
- NAJERIYA A YAU: Dalilin da ’yan Majalisa ke son CBN ya sassauta dokar cire kudi
A jawabin da ta yi wa ’yan sanda ta ce, yarinyar ta ce, “Shi din makwabcin mahaifina ne, ni kuma ina zaune a gidan dan uwanmu.
“Na zo ganin mahaifina sai na tarar ba ya nan, sai na wuce inda ake ajiye makullin na bude.
“Ina shiga sai ga Oba Daddy ya biyo bayana ya rike ni, na ce ya sake ni amma ya ki.
“Haka ya ja ni zuwa wata makarantar firamare, ina ta ihu amma babu wanda ya ji ni.
“Ina kuka, amma haka ya kama ni ta karfin tsiya ya min fyade, daga baya na fada wa marikina, shi ne aka shigar da kara a wajen ’yan sanda,” in ji ta.
An gurfanar da shi ne dai kan zargin yi wa yarinyar mai shekara 14 fyade a ranar 8 ga watan Agustan 2020, wanda hakan ya saba da sashe na 31(2) kundin laifukan yara kanana na Jihar Ekiti na shekarar 2012.
Bayan gabatar da hujojji a yayin shari’ar, alkalin kotun ya gamsu cewar matashin ya aikata laifin da ake tuhumar sa da shi, don haka ya yanke masa da hukuncin daurin rai da rai.