Wata kotun daukaka kara ta yanke wa wani matashi dan shekara 26 hukuncin daurin rai-da-rai bisa laifin kashe mahaifiyar tsohuwar budurwarsa.
Kotun da ke birnin Seoul na kasar Koriya ta Kudu ta samu Lee Seok-joon da laifin daba wa mahaifiyar tsohuwar budurwarsa mai shekara 49 wuka har lahira tare da yi wa dan uwan budurwar mai shekara 14 rauni a gidansu da ke Kudancin birnin a watan Disambar 2021.
- Zazzabin Lassa: Ta kashe183, wasu 1028 sun harbu a Najeriya
- Dattawa Sun Kashe Matashi Domin Tsafi A Zariya
Don haka ta tabbatar da hukuncin daurin rai-da-rai da wata kotun yanki ta yanke wa Lee Seok-joon saboda samun sa da laifin kisan kai da kuma raunata kanin tsohuwar budurwarsa.
Kotun ta gano cewa matashin ya aikata kisan ne bayan da ya badda kama, ya sulale zuwa cikin gidan inda ya yi ajalin mahaifiyar tsohuwar budurwar tasa.
Ya yi wannan aika-aika ne bayan mahaifiyar ta shigar da kara bisa zargin sa da yi wa ’yarta fyade.