✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi jana’izar fasinjoji 19 da motar su ta kama da wuta a Akure

A jiya Lahadi ne aka sallaci gawarwakin mutum 19 da Allah Ya yi wa cikawa sakamakon kamawa da motar su tayi da wuta akan hanyar…

A jiya Lahadi ne aka sallaci gawarwakin mutum 19 da Allah Ya yi wa cikawa sakamakon kamawa da motar su tayi da wuta akan hanyar su ta zuwa Kano daga Legas, an yi wa mamatan sutura aka binne su a garin Akure kamar yadda musulumci ya tanadar.

Mamatan matafiya ne da suka taso daga wata tasha a kasuwar Mil 12 a Legas suka nufi jihar Kano, inda suka gamu da ajalinsu bayan da wata babbar mota mai taya 12 tayo kansu, a lokacin da direban da yake kokarin kaucewa rami, ya yi taho mu gama da motar su ta homa bus inda nan take motocin biyu suka kama da wuta lamarin da ya yi sanadiyar konewar su baki daya, sai direban babbar motar da yaron sa ne kawai suka tsira.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Ondo Femi Joseph ya shaida cewa matukin babbar motar tare da yaron sa sun tsira da ransu inda suka tsere bayan abkuwar hatsarin.