✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi jana’izar Kawu Mala na shirin Dadin Kowa

Marigayin ya rasu sanadiyar ciwon zuciya kamar yadda babban dansa mai suna Anas Aminu ya shaida wa Aminiya.

An yi jana’izar Malam Aminu Muhammad, wanda aka fi sani da Kawu Mala na fim din Dadin Kowa mai dogon zango a tashar Arewa 24 rasuwa.

Al’amin wanda kafin rasuwarsa yake gudanar da sana’ar sayar da magani a unguwar Dakata a Jihar Kano ya rasu ne a ranar Lahadi.

Babban dan marigayin mai suna Anas Aminu, ya shaida wa Aminiya cewa mahaifin nasa ya rasu sanadiyar ciwon zuciya.

“Dama ya dauki kusan shekaru uku yana fama da ciwon zuciya.

“A wannan lokacin kuma da abin ya tashi shi ne ya zo da karar kwana,” in ji dan nasa.

Marigayin ya rasu ya bar mace daya da ’ya’ya goma sha biyu.

A safiyar ranar Litinin din nan ne aka yi jana’izarsa kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada.