Rahotanni sun bulla cewa an sake yi wata haduwar ba zata tsakanin tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da kuma gwamnan jihar na yanzu, Abdullahi Umar Ganduje a birnin Shehu.
Bayanai sun ce haduwar ta gudana ne ranar Lahadi a filin jirgin sama na Sultan Abubakar III da ke Jihar Sakkwato.
Wasu hotunan haduwar da a yanzu sun baibaye dandalan sada zumunta sun nuna yadda cikin raha aka yi musabaha tsakanin Ganduje da Kwankwaso, duk da cewa akwai tsamin dangartaka ta siyasa da ke tsakaninsu.
![](https://i0.wp.com/hausa.dailytrust.com.ng/wp-content/uploads/2022/02/Haduwa-5.jpg?resize=640%2C426&ssl=1)
![](https://i0.wp.com/hausa.dailytrust.com.ng/wp-content/uploads/2022/02/Haduwa-2.jpg?resize=640%2C426&ssl=1)
Aminiya ta ruwaito cewa, ko a watan Agustan bara sai da aka yi irin wannan haduwa ta ba zata tsakanin Kwankwaso da Ganduje a filin jirgin saman kasa-da-kasa na Nnamdi Azikwe da ke Abuja, babban birnin kasar.
Waccan haduwa dai an yi ta ne a yayin da jiga-jigan ’yan siyasar biyu ke tsimayen jirgin da zai yi jigilar komawarsu zuwa Kanon Dabo.