✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi garkuwa dan uwan Mataimakin Gwamnan Edo

Mahara sun yi awon gaba da dan uwan Mataimakin Gwamnan Edo.

Mahara sun yi garkuwa dan uwan Mataimakin Gwamnan Jihar Edo Frederick Shaibu a Benin, babban birnin jihar, Benin.

Tun da aka dauke shi a ranar Litinin masu garkuwar ba su tuntubi iyalansa ba kuma ba a ji duriyarsa ba.

’Yan bindigar “sun farmake shi suka yi garkuwa da shi ne da misalin karfe 7 na safe a yankin Aruogba yayin da je kai ’ya’yansa makaranta.

“Sun yi garkuwa da shi suka bar yaran a inda suka dauke shi amma an sanar da jami’an tsaro.

“Jami’an tsaro na iya bakin kokarinsu na ganin ya dawo cikin iyalinsa ba tare da wani abu ya same shi ba”, cewar majiyar daga cikin iyalansa.

Wakilinmu ya tuntubi Kakakin ’Yan Sandan Jihar Edo, Chidi Nwabuzor, amma ya ce ba shi da cikakken bayanin faruwar lamarin.