✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi garkuwa da ’yan kasuwa da ba a san adadinsu ba hanyar Kano

Duk da rakiyar ’yan sanda da ’yan kasuwar suka samu, sai da ’yan bindiga suka kai musu hari suka yi awon gaba da su.

’Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu ’yan kasuwa da ba a san adadinsu ba a Babbar Hanyar Birnin Gwari zuwa Kano a Jihar Kaduna, suka kuma kashe daya daga cikin ’yan kasuwar.

Ayarin na ’yan kasuwa na hanyarsa ta zuwa fatauci a Kano ne maharan suka tare su a kan a kusa da Dajin Unguwar Yako da ke Jihar Kaduna da misalin karfe 11 na safiyar ranar Laraba.

“Duk da rakiyar ’yan sanda da ’yan kasuwar suka samu, hakan bai hana ’yan bindigar kai musu farmaki ba.

“Sun kashe kashe mutum daya, suka kuma yi awon da ’yan kasuwar da ke hanyarsu ta zuwa Kano daga Jihar Kaduna, wadanda ba a san adadinsu ba,” inji shi, amma ya bukaci a boye sunansa saboda yanayi na tsaro.

Shi ma wani jami’in laifya a garin Birnin Gwari ya tabbatar da aukuwar harin, yana mai cewa matar wani abokin aikinsu na cikin mutanen da aka yi garkuwa da su a harin.

Kokarinmu na samun karin bayani daga Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ya ya ci tura.

Wakilinmu ya kira kakakin rundunar, ASP Jalige Mohammed, amma bai ji duriyarsa ba, har zuwa lokacin da muka kammala hada wannan rahoton.