✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkuwa da wani dalibi a Kaduna

Wadansu da ake zargi masu yin garkuwa da mutane ne sun sace wani matashi kuma dalibin Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Kaduna mai suna Muhammad…

Wadansu da ake zargi masu yin garkuwa da mutane ne sun sace wani matashi kuma dalibin Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Kaduna mai suna Muhammad Kabir.

Dalibin ya bar gidansu ne da ke kan Titin Abuja Road a Rigasa da misalin karfe 7: 30 na safiyar ranar Litinin din da ta wuce a kan hanyarsa ta zuwa makaranta kuma tun daga nan ba a sake jin duriyarsa ba.

Mahaifiyarsa Hajiya Asma’u wadda ta tabbatar da aukuwar sace dan nata ga Aminiya  ta ce a ranar yana azumin Sitta Shawwal.

Ta ce tunda ya fita ba su sake jin doriyarsa ba domin wayarsa na kashe har sai da wadansu suka kira lambar wayar da aka bayar da cigiyarsa a gidan rediyo suka fada wa kanen mahaifinsa yana hannunsu.

“A ranar da safe ya zo ya yi sallama da ni da misalin karfe 7:30, sannan ya wuce wajen mahaifinsa ya gaishe shi a kan zai tafi makaranta.  A ranar da azumin Sitta Shawwal a bakinsa kuma tunda ya fita har zuwa karfe 4:00 na yamma ba mu ji duriyarsa ba sai muka nemi wayarsa amma shiru duk mun kira abokansa da  ’yan ajinsu amma suka ce ai bai je makaranta ba a ranar. Wannan ya sa muke ganin a kan hanya ne abin ya faru da shi,” inji ta.

Ta ce “Bayan an bayar da sanarwa a gidan rediyo aka kuma bayar da lambobin da za a kira idan an gan shi sai wadansu suka kira lambar da aka bayar na kanen mahaifinsa suka ce yana tare da su ko zai so yin magana da shi ne ya ce eh. Sai suka ce za su sake kiransa sannan suka kashe wayarsu don haka yanzu jira ake yi su kira,” inji ta.

Ta yi addu’ar Allah Ya fito da danta cikin koshin lafiya domin a cewarta yaro ne da ba ya da matsala da kowa kuma karatunsa kawai ya fuskanta.

Labarin sace Muhammad Kabir wanda ke karatun fannin kwamfuta  a kwalejin ya yadu a kafafen sada zumunta na zamani musamman Facebook inda jama’a da dama ke ta addu’ar Allah Ya kubutar da shi.