Mahara da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace tsohon dan Majalisar Dokokin Jihar Edo, Fessu Edughele.
Rahotanni sun ce maharan sun yi awon gaba da Honorebul Ubiaja ne a safiyar Litinin, a hanyarsa ta zuwa Benin, babban birnin jihar daga Karamar Hukumar Esan ta Arewa maso Gabas ta jihar.
- Abubuwan da ke jawo salwantar rai ga mata masu juna biyu
- An yi ca kan matar da ta ‘sayar’ da kuli-kulin N1bn
Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Edo, Festus Ebea, ya ce, “An sace Honorebul Ubiaja ne a yankin Ubiaja da ke hanyar Orhionmwon zuwa Benin.
“Ya so ya bi jirgin kasa zuwa Ubeaja, amma hakan bai yiwu ba saboda an dakatar da aikin jirgin Ubeaja zuwa Abuja.”
’Yan bindiga sun sace tsohon dan majalisar ne kwana uku bayan mahara sun yi garkuwa da fasinjoji 32 a tashar jirgin kasa ta Ebeaju da ke jihar zuwa Warri a Jihar Delta.
Festus Ebea ya ce, “Iyalansa sun san an yi garkuwa da shi, an sanar da babban ofishin ’yan sandan yankin, muna fata za su kubutar da shi.”
Wakilinmu ya nemi kakakin ’yan sandan Jihar Edo, SP Chidi Nwanbuzor, domin karin bayani, amma har muka kammala hada wannan rahoton bai amsa kiran ba.