✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkuwa da Shugaban Karamar Hukuma a Filato

An yi garkuwa da Shugaban Karamar Hukumar Kanke da ke Jihar Filato, Honorabul Henry Gotip.

An yi garkuwa da Shugaban Karamar Hukumar Kanke da ke Jihar Filato, Honorabul Henry Gotip.

Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa, da sanyin safiyar Laraba ne wasu ’yan bindiga suka kai hari gidan Shugaban Hukumar da ke Kwang a Karamar Hukumar Jos ta Arewa, suka yi awon gaba da shi.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Filato, Alabo Alfred, da aka tuntube shi kan lamarin, ya ce, zai kira wakilinmu da zarar ya samu cikakken bayani kan lamarin.