✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi garkuwa da mutum 7 lokacin da ake maraba da Gwamnan Taraba

Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace mutum bakwai a hanyar Jalingo zuwa Wukari a jihar Taraba. Rahotanni sun…

Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace mutum bakwai a hanyar Jalingo zuwa Wukari a jihar Taraba.

Rahotanni sun bayyana cewa dukkanin mutanen bakwai ’yan karamar hukumar Ibbi ne, kuma an sace su ne lokacin da suke hanyarsu ta komawa gida daga Jalingo babban birnin jihar, inda suka yi wa Gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku, maraba.

Gwamnan ya dawo Jalingo ne a ranar Alhamis bayan ya kwashe kwanaki 87 ba ya jihar.

Ya samu tarbar mabiyansa da yawa a filin jirgin saman Danbaba Suntai da ke birnin na Jalingo.

Wadanda aka yi garkuwar da su suna cikin wata mota ne kirar bas, kuma an yi garkuwa da su ne bayan sun tsaya a wani shingen binciken ababen hawa, da ke babbar hanyar Wukari da misalin karfe 8:25 na daren ranar Alhamis.