Akalla mutum 17 ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a garin Kuchi na Karamar Hukumar Munya, Jihar Neja, a daren Lahai.
Mahaifan tsohon Shugaban Karamar Hukumar, Yahuza Mohammed, wani dan kasuwa, wani Likita, da wasu mutum 14 ne maharan suka yi awaon gaba da su a garin
- An kashe basarake mako daya bayan garkuwa da shi a Neja
- An cafke basarake a cikin ’yan bindiga a Neja
Majiyar Aminiya ta ce yan bindigar sun ci karfin ’yan bangar garin saboda yawansu, amma ba su kashe ko daya daga cikin ’yan bangar ba.
Ta kara da cewa garin na Kuchi ba shi da jami’in tsaro ko daya, duk da korafin da suka aike na cewar ’yan bindiga na addabar su.
An bayyana cewa Shugaban Karamar Hukumar mai ci, Garba Mohammed Daza ya yi kaura daga garin zuwa Minna, babban birnin Jihar saboda gudun fadawa hannun masu garkuwar.
Wakilinmu ya kira shi a waya don jin ta bakinsa, amma bai amsa wayar tasa ba balle ya yi karin haske dangane da lamarin.
Sai dai, dan majalisar da ke wakiltar mazabar, Andrew Jagaba, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni aka tura jami’an tsaro zuwa yankin.
Ya ce mutane na cikin fargaba, amma ya ba da battacin hukuma za ta ci gaba da kokarin ganin an ceto su baki daya daga hannun ’yan bindigar.