✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkuwa da mutane a Kwalejin Ilimi ta Katsina

An yi garkuwa da ’ya’yan Mataimakin Shugaban Kwalejin da wani basarake.

’Yan bindiga sun kai hari a Kwalejin Ilimi ta Isa Kaita da ke Dutsinma a Jihar Katsina inda suka yi awon gaba da ’ya’yan Mataimakin Shugaban Kwalejin su uku.

Masu garkuwar sun kutsa gidan Mataimakin Shugaban Kwalejinn da ke harabar makarantar ne dauke da makamai, suka tisa keyar ’ya’yan nasa maza uku.

“Ranar Litinin da misalin karfe 11:30 na dare, wasu mutum hudu dauke da muggan makamai suka shiga Kwalejin Ilimi ta Isa Kaita da ke Dutsinma inda suka shiga gidan Mataimakin Shugaban Kwalejin, Dokta Isma’il Ado Funtua, suka yi awon gaba da ’ya’yansa maza su uku.

“Lokacin da suka isa gidan sun samu mai gadin ba ya nan, an dai makala wani kwado a jikin kofar ta cikin gidan, sai suka cire kwadon suka shiga cikin gidan.

“Suna cikin gidan mai gadin ya dawo, suka ritsa shi ya nuna musu mai gidan, amma ya ce ba ya nan.

“Sai suka shiga cikin falo inda suka iske matasan suna karatu, suka yi awon gaba da su tare da mai gadin.

“Amma mutum na hudu a cikin matasan ya samu ya sulale ya tsere,” inji inji majiyarmu da ta nemi a boye sunanta.

Majiyar ta ce a hanya ne masu garkuwar suka saki mai gadin, suka wuce da matasan wadanda dukkanninsu dalibai ne a manyan makarantu.

Mun nemi samun karin bayani daga mai magana da yawun ’yan sanda a Jihar Katsina, Gambo Isa, amma har muka kammala hada wannan rahoto bai amsa kiran wayar da muka yi masa ko rubutaccen sakon da muka tura masa ba.

An sace ’ya’yan Kantoman karamar hukuma

Harin, an kai shi ne bayan da safe ’yan bindiga sun kai hari a wata unguwa Sabuwar Kasa, suka yi awon gaba da ’ya’yan wani mai unguwa su hudu.

Shaidu sun ce ’yan bindigar sun kutsa kda ai ne a yankin Sabuwar Kasa da ke Karamar Hukumar Kafur ta jihar a safiyar Litinin suka yi awon  gaba ’ya’yan wani mai suna Alhaji Hamza Umar.

Alhaji Hamza shi ne Mai Unguwar Sabuwar Kasa kuma Kantoman Karamar Hukumar Funtuwa ta Jihar.