’Yan bindiga sun yi garkuwa da mashawarcin Gwamnan Jihar Sakkwato Aminu Tambuwal kan ayyukka namusamman, Honarabul Sa’idu Muhammad Gumburawa.
Maharan sun tafi da tsohon dan Majalisar Wakilan ne da tsakar dare cikin ruwan sanyi kamar yadda makwabcinsa ya shaida wa Aminiya a garin Gumburawa da ke cikin Karamar Hukumar Wamakko.
- An sace jariri bayan kwana uku da haihuwa
- An cafke boka zai kwakule idanun jariri a Kano
- ’Yan Najeriya miliyan 14.3 ne ke shan miyagun kwayoyi —NDLEA
“Masu garkuwan sun zo ne a babura suka tsallaka gidansa da nufin su tafi da daya daga cikin diyansa kuma sun dauko wanda suka so tafiya da shi uwar yaron ta hana a tafi da shi, sai hatsaniya ta kaure a tsakaninsu abin da ya sanya uban yaron ya fito ya kuma roke su da su tafi da shi su bar yaron, haka aka yi sun tafi da shi ba wata hatsaniya”, a cewar makwabicin.
Kakakin ’yan sandan Jihar Sakkwato, ASP Muhammad Sadik ya ce da misalin karfe 3:30 na dare aka sanar da jami’ansu a Karamar Hukumar Wamakko cewa an sace Honarbul Sa’idu Gumburawa da misalin karfe 3:00.
Ya ce nan take jami’ansu suka zagaye ko’ina sai dai ba su hadu da mutanen ba kuma har zuwa lokacin da Aminiya ta tuntube shi babu wani karin bayani.
Ayyukkan ’yan ta’adda sun kara ta’azzara a Jihar Sakkwato a cikin makon nan inda aka sace mutane da dama a sassan jihar.
Hare-haren ’yan bindiga ya tayar da hankalin al’ummar jihar da halin yanzu suke bukatar dauki daga hukumomin tsaro.