✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkuwa da malaman jami’a biyu a Kaduna

Wasu ‘yan bindiga  da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun yi garkuwa da malaman jami’a biyu a unguwar Mahuta da ke Karamar Hukumar…

Wasu ‘yan bindiga  da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun yi garkuwa da malaman jami’a biyu a unguwar Mahuta da ke Karamar Hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Malaman jami’ar su ne Dakta Adamu Chinoko da Dakta Umar Chinoko duk ‘yan’uwa ne da suke aiki a makarantu daban.

Majiyar Aminiya ta gano cewa, Dakta Adamu Chinoko, malami ne a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya sai Dakta Umar Chinoko, da yake koyarwa a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna.

An yi garkuwan da Dakta Adamu, a daren Alhamis. Yayin da dan uwansa Dakta Umar, ya tafi da Naira Miliyan 2 don biyan kudin fansa shima aka yi garkuwa da shi ranar Lahadi.