Wasu da ake zargin masu zafin kishin addini sun yi garkuwa da wani limamin coci dan kasar Jamus a Bamako, babban birnin kasar Mali.
Wannan dai shi ne karon farko cikin shekaru 10 da aka sace wani dan kasar yammacin duniya a Mali.
- Kotu ta ba da umarnin mayar da Jacob Zuma gidan yari
- Kasashe 10 da ka iya lashe Gasar Kofin Duniya ta bana
Kawo yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin yin garkuwa da limamin cocin, wanda ya shafe fiye da shekaru 30 a Mali.
Sai dai Gidan Rediyon Jamus ya ruwaito cewa tuni aka dora zargi kan kungiyar IS mai tarihin garkuwa da ’yan kasashen waje don neman kudin fansa.
Rahotanni sun ce an gano motar Hans-Joachim Lohre a Bamako, babban birnin kasar Mali kusa da makarantar da yake koyarwa.