✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi garkuwa da kwamishina a Kuros Riba 

Maharan sun yi awon gaba da ita ta karfin tsiya.

Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da Kwamishinar Harkokin Mata ta Jihar Kuros Riba, Gertrude Njar, a ranar Laraba a Kalaba.

Wani ganau, Mista Samuel Okon ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeria (NAN) cewa wasu mutane rufe da fuska ne suka dauke ta daga motarta ta karfin tsiya.

A cewar Okon, sun tafi da kwamishinar ne a cikin motarsu, inda suka bar motarta a kan hanya.

Mista Kalita Aruku, mai bai wa Gwamna Ben Ayade shawara kan harkokin yada labarai, ya tabbatar wa NAN faruwar lamarin.

“Gaskiya ne, jami’an tsaro sun sanar da mu cewa an yi garkuwa da kwamishinar harkokin mata.

“Jami’an tsaro sun fara farautar wadanda suka sace ta da nufin kubutar da ita ba tare da ta ji wani rauni ba,” in ji shi.