’Yan bindiga sun yi garkuwa da Kwamishinan Gidaje da Raya Birane na Jihar Binuwai, Dennis Ekpe Ogbu, a hanyar Ado-Otukpo da ke jihar.
An yi garkuwa da kwaminishan ne da milsain karfe 9 na dere, a hanyarsa ta zuwa mahaifarsa a Karamar Hukumar Ado, inda maharan suka tsayar da motarsa da karfin bindiga suka yi awon gaba da shi.
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Kona Ofisoshin INEC A Kudu Zai Haifar
- An kashe babban dan sanda a rikicinsu da sojoji a Legas
- Qatar 2022: Birtaniya ta kora Senegal gida da ci 3-0
Da take tabbatar wa Aminiya da faruwar lamarin, kakakin ’yan sandan jihar, SP Catherine Anene, ta ce, “Tabbas an yi hakan, yanzu muna hanyarmu ta zuwa wurin, nan gaba zan ba ku karin bayani.”
Matsalar garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa ta zama ruwan dare a sassan Najeriya, duk kuwa da kokarin jami’an tsaro na yakar bata-garin da nufin kawo karshen matsalar.
Aminiya ta kawo rahoton yadda a Jihar Katsina, ’yan binidiga suka yi garkuwa da mutum 46 ciki har da dalibai da mata da masu sallah a masallaci a kananan hukumomin Batsari da Funtua.
A halin yanzu dai batun sha’anin tsaro na daga cikin abubuwan da masu yakin neman zaben 2023 suke mayar da hankali a kai.