✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkuwa da hamshakin dan kasuwa a Kebbi

Wasu ‘yan bindiga sun yi  garkuwa da hamshakin dan kasuwa Alhaji Murtala Zauro wanda yake zaune a Birinin Kebbi ranar Asabar. Iyalan Alhaji Murtala Zauro…

Wasu ‘yan bindiga sun yi  garkuwa da hamshakin dan kasuwa Alhaji Murtala Zauro wanda yake zaune a Birinin Kebbi ranar Asabar.

Iyalan Alhaji Murtala Zauro sun bayyana wa majiyar mu cewa, masu garkuwan sun dakatar Zauro lokacin da yake cikin motarsa mintuna kadan bayan ya halarci sallar isha’i.

Lamarin ya auku ne a unguwar su dake Zauro a hanyar Argungu a Birnin Kebbi jihar Kebbi.

Alhaji Zauro dai dan kasuwa ne a babbar kasuwar Birnin Kebbi.

Jami’in hulda da jama’a na Hukumar ‘yan sandan jihar Kebbi, DSP Danjuma Possi ya tabbatar aukuwar lamarin.