✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkuwa da dan Kwamishina a Bayelsa mai shekara 6

Wasu ‘yan bindiga a daren ranar Lahadi sun kai hari gidan Kwamishinan albarkatun ruwa na jihar Bayelsa Mista Nengi Talbot, sannan suka yi garkuwa da…

Wasu ‘yan bindiga a daren ranar Lahadi sun kai hari gidan Kwamishinan albarkatun ruwa na jihar Bayelsa Mista Nengi Talbot, sannan suka yi garkuwa da dansa mai shekara shida mai suna Antonio.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da yin garkuwa da dan Kwamishinan Bayelsa lokacin da ‘yan bindigar suka shiga gidan da ke rukunin gidaje na Opolo axis a cikin Yenagoa babban birnin jihar da misalin karfe na 10:30 na dare ranar Lahadi.

Har zuwa yau ‘yan bindigar basu bukaci komai ba kuma ba a san inda suka yi da yaron ba don biyan kudin fansa. Kamar yadda kamfanin dillancin labarai NAN ya sanar.