Jama’ar gari sun yi murna da farin ciki yayin da bayanai suka tabbatar cewa, Sarkin Kajuru Alhaji Alhassan Adamu, wanda ’yan bindiga suka yi awon gaba da shi ya kubuta.
Sai dai majiyar ta ce har yanzu ba a sako sauran mutum 13 da aka sace tare da sarkin ba.
- Rundunar sojin sama za ta dauki sabbin hafsoshi aiki
- Masu garkuwa da Sarkin Kajuru na neman N200m a matsayin kudin fansa
“’Yan bindigar sun saki sarkin ne a kewayen wasu dazuzzuka da ke kaiwa zuwa ga masarautarsa,” a cewar majiyar.
Wani daga cikin iyalan gidansa ya ce sarkin yana cike da koshin lafiya yayin da ya dawo, amma za su kai shi asibiti domin likitoci su tabbatar da hakan.
Sakin basaraken na zuwa ne bayan da ’yan bindigar suka nemi a biya su fansar naira miliyan 200 kafin su sake shi tare da sauran mutanen da suka sace.
Ya zuwa yanzu dai babu wasu cikakkun bayanai dangane da biyan fansar ko kuma sabanin haka.
Aminiya ta ruwaito cewa, wani daga cikin masu nadin Sarkin Kajuru ne ya tabbatar cewar ’yan bindigar sun tuntube su domin gabatar da bukatarsu ta karbar kudin fansa.
Basaraken ya fadi hakan ne a yayin da ya ce suna ci gaba da tattaunawa da ’yan bindigar da zummar ganin an kubutar da Sarkin da kuma jama’arsa daga hannun mutanen da suka yi garkuwa da su.
Rahotanni sun ce Sarki Adamu ya shaida wa jami’an tsaro barazanar da suke fuskanta sa’o’i 48 kafin ’yan bindigar su kai musu hari.
Tun a Juma’ar da ta gabata ce Sarkin ya gana da jami’an tsaro inda ya shaida musu barazanar da yake fuskanta.
A kan haka ne wani jami’in gwamnati ya ce Kwamandan Sojin da ke yankin ya bai wa Sarkin shawara dangane da zirga-zirgar da yake da kuma bukatar kara sanya ido.