An shawarci gwamnatocin Najeriya da su dawo da koyar da ilmin tarihi a makaratu tun daga matakan karamar hukuma har zuwa ga Gwamnatin Tarayya.
Ferfesa Isma’ila Abubakar Tsiga na Sashen Harshen Ingilishi na Jami’ar Bayero, Kano ne ya bayar da wannan shawara a cikin wata makala da ya gabatar a wajen bikin tunawa da shigowar karatun boko a kasar Hausa.
Taron, wanda yake na hadin gwiwa ne tsakanin Sashen Nazarin Harsunan Najeriya na Jami’ar Umar Musa da na Sashen Nazarin Harsunan Afirika na Jami’ar Cairo da ke kasar Masar mai taken: ‘Waiwayen karni daya Na Boko A kasar Hausa’ tare da kaddamar da littafin ‘Ruwan Bagaja A Ma’aunin Masana’ an gudanar da shi a dakin taro na Jami’ar Umar Musa, a ranar Asabar ta makon da ya gabata.
Shehin malamin wanda ya yi bayani mai tsawo a kan tarihin karatun boko a kasar Hausa, ya ce: “kalubalantar da malaman addinin Musulunci na kasashen Hausa da suka yi wa yanayin karatun ya sa suka rika cewa, za a koyar da karatu ko za a yi ‘Biri Boko?’ wanda aka cire sunan ‘Birin’ aka dauki ‘Bokon’ ya koma karatu ko rubutun book; wanda ake faro shi daga hagu zuwa dama, sabanin na ajami da ke farawa daga dama zuwa hagu.” Ferfesan har ila yau, ya ba da shawarar a kafa wata cibiyar da za ta rika yin nazari a yankunan Sahara. “Dangane da batun bayar da ilmin boko ga almajirai, ina ganin a dauki ginannar makarantar firamare daya a yanki, a mayar da ita ta Larabci maimakon kashe makudan kudi wajen gina wata sabuwa.”
Ya kara da cewa, a koyar da dalibai a harsunansu na gida zai yi matukar tasiri fiye da na wani harshen; inda ya ba da misali da wata matsala da ya samu da na’urarsa mai kwakwalwa a wajen fassara kalmar ‘Hausaland’ inda ta fassara masa kowane daban-daban, sabanin a dunkulen fassarar da yake tunani.
Shi kuwa jagoran masu bincike, Farfesa Aliyu Muhammadu Bunza na Sashen Nazarin Harsunan Najeriya a Jami’ar Umaru Musa da ke Katsina, ya bayyana makasudin yin wannan biki a kan abubuwa uku. “Na farko, yin hidimar barka da arziki da cikar littafin Ruwan Bagaja shekaru 80 (1933-2013). Na biyu, tabbatar wa duniya dogon zamanin da karatun boko ya yi a kasar Hausa. Na uku, gabatar da ayyukan da masana 52 suka yi a kan littafin Ruwan Bagaja mai taken: ‘Ruwan Bagaja A Ma’aunin Masana.” Inji shi
Farfesa Bunza ya ce sun kirkiro da gawurtacen bincike na kasa da kasa mai taken: ‘Bil Adama A Yankin Sahara Na Duniya: Bincike Na Musamman A Kan Bil Adama’ wanda hadin gwiwar Jami’ar Cairo da ta Umaru Musa. Malamin nazarin harsunan ya kara da cewa: “Babbar manufarmu ita ce Hausa ta kasance kanwa a koyaushe ake zancen harsunan Najeriya a fagen ilmi. kudirinmu Hausa ta kasance harshen koyar da boko, samawa Hausa nagartaccen bagire a jami’o’inmu da cibiyoyin nazarin harsuna da al’adu a duniyar ilmi.”
Farfesan ya tunasar da malaman Hausa da manazartanta da su sani Hausa ba ta san kowa ba sai su. Ya ce tuni suka fara tuntubar jami’o’in Afrika Ta Yamma don kulla zumuncin koyar da Hausa a kasashensu. “Da yardar Allah Jami’ar Umaru Musa ’Yar’aduwa za ta fara ba da gudunmuwarta na koyar da digirin-digirgir a Hausa,” inji shi.
Farfesa Balarabe Zulyadaini shi ne ya yi bitar littafin na Ruwan Bagaja, yayin da Farfesa Muhammad Lawal Aminu ya kaddamar da littafin karkashin jagorancin taron, wanda Injiniya Musa Abdullahi, Sa’in Katsina da Wakilin Tarihi na Daura suka wakilci sarakunan Katsina da Daura. Gwamnan Jihar Katsina Barista Ibrahim Shema ya samu wakilcin mai ba shi shawara ta fuskar Difilomasiya Sada Ruma.
Daga cikin wakillan jami’o’in da suka halarci wannan taro baya ga na gida, akwai na Jihar Tawa da Zinder daga Jamhuriyar Nijar da Wagadugu kuma na kasar Barkina Faso. Akwai Farfesoshin Hausa a Najeriya akalla 30, inda Jami’ar Bayero ta Kano ke da 12 daga cikinsu,sai Jami’ar danfodiyo Sakkwato na da 6. Ita kuma Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya na da 5, ta Maiduguri na da 4, Jami’ar Jihar Kaduna, Nasarawa Keffi da ta Umaru Musa a Katsina na da guda-guda.
An yi bikin tunawa da zuwan karatun boko kasar Hausa
An shawarci gwamnatocin Najeriya da su dawo da koyar da ilmin tarihi a makaratu tun daga matakan karamar hukuma har zuwa ga Gwamnatin Tarayya.Ferfesa Isma’ila…